Akwati na karkashin gado na na dauke da wasiku 47.duk sun fara da kalma daya (masoyiya) Amma Babu daya da ta taba ganin hasken rana Babu daya da ta taba karantawa.
Na hadu da ita a shekarar 2016, sunanta bazan fada ba amma zamu kirata aisha.ba itace mafi kyawon yarinya a ajinmu ba,amma murmushinta na da iKon kashe damuwa ta.lokacin da take dariya idanuna na rufe kansu.
Matsalar itace ni yaro ne mai kunya.mai talauci, uniform Dina ya tsufa,takalma na sun yage.kullum Ina ganin samari masu kudi suna mata magana.ni kuma na zabi nayi mata magana a takarda.
Kowace dare bayan karatu, ina dakko takarda in rubuta mata.na rubuta mata game da mafarkina.na rubuta mata yadda zuciya ke bugu idan ta wuce kusa Dani.na rubuta mata cewa wata rana zan zama mutumin kirki inzo gidansu na nemi aurenta.wasiku 47 kenan a shekaru biyar.
A zuciyata inacewa, idan na kammala karatu na samu aiki, zan bata su duka. ta karanta tasan nasota tunda dadewa.
Shekaru sun wuce.na kammala karatu.nasamu karami aiki a jos.na Tara kudi na sayi sabon kaya.A ranar da na yanke shawarar inje innemo ta,sai kawai kawarta ta kirani a waya.
"Kaji abinda ya faru da Aisha"?ta tambaya.
Zuciya ta fadi. "Me ya faru"?
"A sati biyu da suka wuce akai aurenta tana kano yanzu tare da mijinta".
Wayar ta fadi daga hannuna.shekaru 5 na wasiku.shekaru 5 na mafarki.shekaru 5 na tsoro.duk sun zama a banza cikin dakika 10.
Daga yanzu duk lokacin da bude akwatin nan sai naji kalmomin da ban fada ba sunamin nauyi.na gane cewa tsoro babban barawo ne.ya sace min shekaru 5 na farinciki.ya sace min damar da zan iya samu da ita.
Don haka,idan kana karanta wannan,Kuma akwai wani da kake so,don allah kayi magana Yau.ka tura sakon,ka kira waya. ka fadi "inasonki".
Domin wasikar da ba'atura ba itace wasika mafi nauyi a duniya.Ba takardace ke dauke ba zuciyace ke dauka.kuma tana yin nauyi kowace rana har abada.
Nadama daga baya tamkar maganinda akasha bayan mutuwane baida wani amfani.
You must be logged in to post a comment.