Shin an tura ka jihar da baka so a NYSC 2026? Kada ka damu, akwai hanyar da zaka koma jihar da kake so wanda ake kira NYSC Relocation ko Redeployment. A cikin wannan labarin zan nuna muku yadda zaku yi shi da waya kawai ba tare da kun biya wani N10,000 ba.
Mutane da yawa suna biyan wasu mutane kudi don su yi musu relocation, amma gaskiya zaka iya yi da kanka kyauta a camp ko bayan camp.
LOKUTA 2 DA AKE YIN RELOCATION:
1. A Cikin Camp (Within Camp): Wannan shi ne mafi sauki. Kana cikin camp ne zaka nemi relocation. Idan sun amince, ba za ka yi aiki a jihar da aka tura ka ba, za su tura ka wata jihar kai tsaye.
2. Bayan Camp (After Camp): Idan ka kammala camp, zaka iya neman relocation a NYSC portal. Wannan kuma yana yiwuwa amma yana daukan lokaci kadan.
WANE NE YA CANCANTA A YI MASA RELOCATION?
NYSC ba sa amincewa da kowa sai da dalili mai karfi. Ga dalilai 3 da suke amincewa da su 100%:
Dalili na 1 - Marital Ground (Ga Mata Masu Aure): Idan ke mace ce mai aure, NYSC za su tura ki wurin mijin ki. Abinda ake bukata shine Marriage Certificate, da takardar canjin suna a jarida, da kuma ID card na mijin ki ko utility bill dinsa. Wannan shine dalilin da yafi kowanne sauki.
Dalili na 2 - Health Ground (Lafiya): Idan kana da wata cuta ko rashin lafiya da ke bukatar ka kasance kusa da asibiti ko gida. Dole ka je ka ga doctor a camp, likitan zai baka report. Kada ka karya karya takarda, saboda suna bincike sosai yanzu.
Dalili na 3 - Security Ground (Tsaro): Idan jihar da aka tura ka akwai matsalar tsaro sosai kuma baka jin dadin zama a wurin. Wannan ma NYSC suna kallonsa.
YADDA ZAKA NEMI RELOCATION DA WAYA:
Mataki na 1: Shiga NYSC Portal wanda shine portal.nysc.org.ng da wayar ka.
Mataki na 2: Ka shiga da email da password dinka.
Mataki na 3: Ka danna Relocation. Za su tambaye ka dalilin da yasa kake son komawa.
Mataki na 4: Ka zabi jihar da kake son zuwa. Ka zabi jihohi 3 da kake so.
Mataki na 5: Ka saka takardun ka kamar marriage certificate ko medical report.
Mataki na 6: Ka danna Submit.
Idan kana cikin camp, ka je ka ga Camp Director ko Relocation Officer a camp. Ka basu takardun ka da kuma application letter. Suna amincewa a cikin kwana 2 zuwa 3.
SHAWARA TA KARSHE:
Kada ka biya kowa kudi a camp don ya yi maka relocation. Mutane da yawa suna damfarar corpers. Yi da kanka kyauta. Kuma idan an tura ka wata jiha da baka so, ka yi hakuri ka je camp din farko, a can ne zaka nemi relocation, ba a gida ba.
Idan kina mace mai aure, ki tabbata kin dauki original da photocopy na marriage certificate dinki da na mijin ki.
Allah ya sa a yi NYSC lafiya.
You must be logged in to post a comment.