Yadda Ake Samun Loan Na N50,000 A Opay Da PalmPay Da Waya Kawai A 2026

Follow
Listen to Article Listen to this article read aloud

Audio uses the voice available in your browser or device.

A yau na zo muku da labarin da zai taimaka muku sosai idan kuna cikin bukatar kudi na gaggawa. Dukkan mu mun san cewa rayuwa tayi tsada yanzu kuma wani lokaci mutum yana bukatar karamin kudi don ya cike wata bukata. Opay da PalmPay yanzu suna bayar da loan har N50,000 zuwa N500,000 da waya kawai ba tare da ka je banki ba.

 

Ni kaina na karbi loan na N20,000 a PalmPay makon da ya wuce kuma zan nuna muku yadda na yi.

 

OPAY LOAN - YADDA AKE KARBA:

 

Opay tana da abin da ake kira OKLoan ko EasyCash wanda yake cikin Opay App din.

 

Abinda zakayi:

1. Ka bude Opay App dinka. Idan baka da shi, ka sauke a Playstore ka bude account da NIN dinka.

 

2. Da zarar ka shiga, zaka ga wuri da aka rubuta LOAN ko OWealth. Ka danna shi.

 

3. Opay za su duba yadda kake amfani da account dinka. Idan kana yawan saka kudi da kuma yin transfer da shi, za su baka loan da sauri. Idan sabon account ne, za su fara baka N3,000 zuwa N5,000.

 

4. Ka zabi adadin da kake so, misali N10,000. Za su nuna maka kudin ruwa da kuma ranar da zaka biya. Kudin ruwa na Opay daga 5% zuwa 15% ne.

 

5. Ka danna Apply. Idan suka amince, kudin zai shigo account dinka a cikin minti 5.

 

PALMPAY LOAN - YADDA AKE KARBA:

 

PalmPay ma tana da nata loan din. Ita ta fi Opay bayar da kudi da yawa.

 

Abinda zakayi:

1. Ka bude PalmPay App dinka.

 

2. Ka je wurin da aka rubuta Loan ko Finance.

 

3. PalmPay za ta bukaci ka cike bayananka kamar NIN, BVN da kuma hoton ka. Wannan don tabbatar da kai ne.

 

4. Bayan ka cike, za su baka loan bisa la'akari da yadda kake amfani da PalmPay. Ni na fara da N5,000, bayan na biya na samu N20,000, yanzu sun kai ni N50,000.

 

5. Kudin na shigowa nan take.

 

YADDA ZAKA BIYA KUMA KA KARA SAMUN BABBAN LOAN:

 

Sirrin samun babban loan a Opay da PalmPay shine ka biya akan lokaci. Idan ka karbi N5,000 ka biya a cikin kwana 7 ko 14, za su kara maka zuwa N10,000, sannan N20,000, har ka kai N100,000.

 

Kada ka karbi loan ka ki biya, saboda za su saka ka a blacklist kuma ba za ka sake samun loan a ko'ina ba a Nigeria. Kuma za su kira lambobin mutanen da ke wayar ka.

 

GARGADI:

 

Kada ka karbi loan da yawa a lokaci daya a apps da yawa. Ka fara da daya, ka biya, sannan ka karbi wani. Kuma ka karanta kudin ruwa kafin ka karba.

 

Wannan loan din ya dace da mutane masu kananan kasuwanci da dalibai da ke bukatar kudin cefane.

 

Ka gwada

yau kuma ka gaya min a comment nawa suka baka.

More Articles by This Writer

Support the Writer

Enjoyed this article? You can support the writer with a voluntary donation.

Your donation supports Amina tukur

Minimum donation: $2.00   •   90% of the donation is allocated to the writer after the LodPost commission.

Comments

You must be logged in to post a comment.

About Author

0 Followers
0 Following
13 Articles
1 Likes