Yadda Na Samu Data Mai Rahusa a MTN, Airtel da Glo Da Waya Kawai - Cikakken Bayani 2026

Follow
Listen to Article Listen to this article read aloud

Audio uses the voice available in your browser or device.

Assalamu Alaikum jama'a, yau na zo muku da labari mai amfani wanda zai taimaka muku sosai musamman mu da muke amfani da waya kawai wajen hada-hada a internet. Dukkan mu mun san data yayi tsada yanzu, amma akwai hanyoyi na samun data mai rahusa wanda mutane da yawa basu sani ba.

 

A cikin wannan labarin zan nuna muku yadda na samu data mai rahusa a MTN, Airtel da kuma Glo da waya ta kawai.

 

FARKO - MTN CODE MAI RAHUSA:

 

MTN ita ce babbar hanyar sadarwa a Nigeria kuma suna da tayi na musamman da ake kira MTN4ME. Wannan tayin ba kowa yake samun iri daya ba, kowane layi da nasa ne.

 

Abinda zakayi shine ka danna *121# a wayar ka. Da zarar ka danna, za su nuna maka menu. Ka zabi Data4ME. A nan ne za ka ga offer na layin ka. Ni kaina na samu 1GB da N200 na kwana 30 a wannan wurin. Wasu mutane ma suna samun 2GB da N500 ko 4GB da N1000.

 

Idan *121# bai kawo maka tayi mai kyau ba, ka gwada sabon code na MTN wanda shine *312#. Wannan shine sabon code din da MTN ta sauya daga *131#. A *312# zaka ga dukkan data plan na MTN. Hakanan ka gwada *312*100# kai tsaye don 1GB da N200.

 

Akwai kuma tayin dare na MTN. Ka danna *406# ka koma MTN Pulse, sannan ka danna *406*3# don data na dare. Zaka samu 250MB da N25, 500MB da N50 daga karfe 11 na dare zuwa 6 na safe. Wannan ya fi dacewa da mu da muke so mu sauke film da daddare.

 

BIYU - AIRTEL CODE MAI RAHUSA:

 

Airtel ma suna da nasu tayin. Ka danna *312# ko *121*1#. A Airtel zaka iya samun 1GB da N300 na kwana 30 da kuma 2GB da N500. Hakanan suna da data na dare mai rahusa sosai, 1GB da N100 daga 12am zuwa 5am. Ka danna *312# ka zabi Night Bundle.

 

UKU - GLO CODE MAI RAHUSA:

 

Glo ita ce ta fi kowa bayar da data mai yawa. Ka danna *312# a layin Glo. Glo tana bada 2GB da N500 na satin daya. Kuma idan ka sake kunnawa, suna kara maka bonus. Glo kuma tana da 1GB da N300 na dare.

 

SHAWARA TA KARSHE:

 

Kada ku yarda da duk wani link da ke cewa zai baku 15GB kyauta idan kun danna. Duk scammers ne. Yi amfani da USSD code kadai.

 

Kuma ku sauke myMTN App, myAirtel App da kuma Glo Cafe App a Playstore, saboda suna bada data kyauta ga sabbin masu amfani. MTN tana bada 500MB, Airtel tana bada 1GB kyauta idan ka sauke app din a karon farko.

 

Ku gwada wadannan code din yau kuma ku gaya min a comment abinda kuka samu a

layin ku. Allah ya taimaka.

More Articles by This Writer

Support the Writer

Enjoyed this article? You can support the writer with a voluntary donation.

Your donation supports Amina tukur

Minimum donation: $2.00   •   90% of the donation is allocated to the writer after the LodPost commission.

Comments

You must be logged in to post a comment.

About Author

0 Followers
0 Following
13 Articles
1 Likes