A sati biyu da suka wuce, na fada muku labarin bakin ciki na na asarar N50,000 a Telegram danayi da kuma yanda na fara farfadowa da N500 na data. Mutane da yawa sun turo min da sako a WhatsApp suna cewa, ka fada mana gaskiya, yanzu haka da ka samu kudi, rayuwarka ta canza yaya? Yau na yanke shawarar zan fada muku komai ba tare da boye komai ba, abin da ya faru da ni a kwana 30 da suka wuce bayan na rike Lodpost da gaske.
Gaskiya bayan na biya bashin N20,000 da na aro, na samu kaina da N0 a aljihu na, amma zuciyata a kwance take saboda na rabu da bashi. A rana ta farko bayan biyan bashin, na zauna na yi wani sabon plan, nace a wannan karon ba zan yi aiki don kudi kawai ba, zan yi aiki don in gina sunana domin na fahimci cewa a duniyar online, sunanka ya fi kudi daraja.
A cikin kwana 30 din nan, na koyi abubuwa da dama da suka canza tunanina gaba daya.
Na farko, na koyi cewa da safe ake samun nasara. A baya ina tashi da karfe 9 ko 10 na safe ina tashi ina duba status kawai amma a kwana 30 din nan na canza lokacin tashi, ina tashi da karfe 5 na safe, ina alwala ina sallah, sannan ina daukar wayata ina rubuta labari daya kafin kowa ya tashi, na lura duk labarin da na rubuta da karfe 5 zuwa 6 na safe, yakan samu views ninki uku na wanda na rubuta da rana, saboda mutane da yawa idan sun tashi da safe, abu na farko da suke yi shine bude Facebook da Google idan labarinka yana wajen, zasu ganshi.
Na biyu, na koyi sirrin Facebook Groups. A da ina posting a profile dina kawai, ina samun likes 10. Amma wani bawan Allah ya koya min cewa akwai groups a Facebook da mutane dubu 100 suke ciki. Kuma suna bukatar labarai, naje na shiga groups guda 15 na Hausawa kullum bayan na rubuta labari, ina shiga kowane group na saka labarin tare da wani rubutu mai jan hankali, a rana daya ina samun mutane 500 zuwa 1000 suna shiga labarina daga Facebook Groups kadai. Wannan shine babban sirrina da ban taba fadawa kowa ba sai yau.
Na uku, na koyi yadda ake amsa comment. A da idan mutum yayi comment a labarina, bana amsawa, ina ganin kamar ai ya karanta ya wuce Kenan amma yanzu na gane cewa duk mutumin da yayi comment yana kara yada labarina ne ga wasu, don haka yanzu duk wanda yayi comment, ina amsa masa cikin minti 5. Ina ce masa na gode, ina yi masa tambaya. Idan mutane 20 suka yi comment kuma na amsa su duka 20, Facebook da Lodpost zasu dauki labarina a matsayin labari mai muhimmanci su kara yada shi.
Na hudu, na koyi darasi akan kada in kwatanta kaina da kowa. A kwana 30 din nan, akwai abokina wanda yake samun N5000 a rana. Ni kuma wata rana ina samun N200, da farko na ji haushi na ce ai ni ma ina rubutu sosai, amma daga baya na fahimci kowa da lokacin shi, shi ya fara shekara daya da ta wuce ni kuma wata daya kawai na yi, don haka na daina maida hankalina akansa, na mayar da hankali kan nawa. Na rika cewa a kowace rana zan fi jiya. Wannan tunanin ya bani kwanciyar hankali.
A karshe, abu na biyar da ya canza rayuwata a kwana 30 din nan shine na fara adana kudi. A baya duk N500 da na samu ina cinye shi da data, amma yanzu na raba kudina gida uku, Kashi daya na data, kashi daya na ajiya, kashi daya na sadaka ga iyayena. Duk da kudin karami ne, amma wannan tsarin ya koya min darajar kudi.
A yau, bayan kwana 30, na samu abubuwa da yawa. Na farko na samu kusan N32,000 a Lodpost kadai, Na biyu na samu followers sama da 800 da suke jiran labarina kullum, Na uku na samu kwanciyar hankali, ban sake jin tsoron rasa kudi ba saboda na san yadda ake samu na halal.
Don haka kai da kake karanta wannan labarin kuma kana cikin damuwa, ina son in fada maka cewa, ba kai kadai bane, nima na shiga damuwar amma mafita tana nan, kada ka daina ka tashi da safe, ka rubuta, ka yada, ka amsa mutane, ka yi hakuri watarana zaka yi murmushi kamar yadda nake murmushi ayanzu.
Idan wannan labarin ya karfafa maka gwiwa, ka tura wa wani da kake ganin yana cikin irin halin da na shiga, kuma ka fada min a comment section, wane mataki kake ciki yanzu? Shin kana cikin asara ne ko kana cikin farfadowa?
Allah ya bamu sa'a.
Bayan Na Farfado Daga Asarar N50,000, Ga Yadda Rayuwata Ta Canza Cikin Kwana 30 A Lodpost
Support the Writer
Enjoyed this article? You can support the writer with a voluntary donation.
Your donation supports
Muhammed
You must be logged in to post a comment.