Bayan Na Yi Asarar N50K, Ga Abinda Nayi Na Samu N15,000 A Mako Daya – Ba Tare Da Saka Sisi BA

Follow

A labarina na baya na fada muku yadda na yi asarar N50,000 a hannun yan damfara ta Telegram da suka ce zasu ninka mun kudina, mutane da yawa sun tambaye ni a comment cewa bayan kayi asarar to me ka yi? Ta yaya ka farfado? Yau zan fada muku gaba daya abin da na yi mataki-mataki wanda ya mayar da ni hayyacina da taimakon Allah.
Bayan an yi min damfara, gaskiya na shiga damuwa mai tsanani, na kwana biyu ban ci abinci yadda ya kamata ba, wayata na kashe saboda kunya, na ci bashin abokina N20,000 a cikin N50,000 din, ina tunanin yadda zan biya shi. Na yi kuka a daki amma a rana ta uku, na zauna na yi wa kaina Magana na ce wannan kukan ba zai mayar da kudin ba dole ne in tashi in nemi mafita.

Mataki na 1: Na daina bin duk wani abu na ninka kudi.
Abu na farko da nayi shine na fita daga dukkan group din Telegram da WhatsApp na ninka kudi, Crypto signal, da Forex. Na goge su duka a wayata. Na fahimci cewa babban dalilin damfaara na shine kwadayi na. Idan ban kashe kwadayin nan ba, zan sake fadawa.
Mataki na 2: Na koma neman ilimi na gaskiya.
Na shiga YouTube na rubuta "yadda ake samun kudi a online ba tare da jari ba". Na kalli bidiyo kusan 20. Duka suna magana akan abubuwa 3: Lodpost, SproutGist da rubutu. Na zabi Lodpost saboda ba ya bukatar kudi, kawai rubutu. Na koyi yadda ake bude account, yadda ake rubutu da yadda ake saka hoto.
Mataki na 3: Na fara da abin da ke hannuna.
Ba ni da kudi sai N500 data. Na sayi data na fara rubutu. Labarina na farko bai samu views 15 ba, naji haushi amma na cigaba, na rubuta na biyu, na uku, na dinga yadawa a WhatsApp status, a group din makaranta, a Facebook. A rana ta 4 na samu N150. Na yi farin ciki kamar na samu miliyan saboda kudi ne na halal da na sha wahala a kai.
Mataki na 4: Na mayar da hankali kuma na hakura.
Na yanke shawara zan rubuta labari daya kullum na tsawon kwana 30 ba tare da tsallakewa ba. Ko da babu views zan rubuta wannan hakurin shine ya bani nasara. A mako na biyu na fara samun N400, N600 a rana. A mako na uku na biya bashin N20,000 na da na aro. A wata na biyu na samu N18,000 a Lodpost kadai.
Yanzu haka ina rubuta muku wannan labarin ne daga kudin data da Lodpost ya bani ban sake fadawa damfara ba.
Don haka abokina da kake karanta wannan kuma kayi asara kamar ni, kada ka karaya asara ba karshen duniya ba ce. Kuskure ne da kowa ke yi amma abin da ya fi muhimmanci shine ka tashi ka gyara. Ka daina kuka ka fara aiki.
Idan na iya farfadowa bayan asarar N50,000, kai ma zaka iya. Fara yanzu, ka bude Lodpost, ka rubuta labarinka na farko ko da N100 ka samu, ka fara.
Allah ya mayar mana da alheri.
Ka taba farfadowa bayan asara? Ka fada mana a comment mu karfafa juna.

More Articles by This Writer

Support the Writer

Enjoyed this article? You can support the writer with a voluntary donation.

Your donation supports Muhammed

Minimum donation: $2.00   •   90% of the donation is allocated to the writer after the LodPost commission.

Comments

You must be logged in to post a comment.

About Author

1 Followers
1 Following
3 Articles
3 Likes