Limamin Masallacin Mu Ya Mutu Da Asubahi, Amma Abin Da Ya Fada Jiya Da Dare Ya Girgiza Garin Mu Baki Daya

Follow
Listen to Article Listen to this article read aloud

Audio uses the voice available in your browser or device.

Jiya da dare bayan Sallan Isha'i, Limamin masallacin mu ya kira mu mu matasa guda bakwai, ya ce yana da Magana mun dauka zai yi mana wa'azi kamar kullumne amma abin da ya fada ya sanya mu duka kuka.
Yace, "Yara na, na yi mafarkin mutuwa jiya da dare, na ganane lokacina yayi, amma abin da ya fi tsorata ni ba mutuwar bace, abin da mutane za su tuna da ni da shi ne."
Sannan ya ce, "Don haka ina son in baku abubuwa biyar da mutane suke danasani a lokacin mutuwarsu don kada ku fada cikin nadama irin tata."
1. Mutane suna danasani saboda sun bata lokaci suna fushi da mutane.
Yace, "Na ga mutane da yawa sun kwana suna fushi da dan uwansu saboda N500, saboda magana daya, amma a lokacin mutuwa sai su gane cewa wannan fushin bai da amfani ku yafe yau da dare ku kira duk wanda kuke fushi da shi ku yafe masa domin baka san waye zai kwanta baza’a waye gari dashi ba."
2. Suna yin danasani saboda basu amfanar da lokaci da iyayensu ba.
Yace, "Na ga wani mutum yana kuka a lokacin mutuwarsa yana cewa, 'Na kasance ina da kudi, amma ban taba zama da mahaifiyata na ci abinci tare ba'. Yara, ku dawo gida. Ku ci abinci da iyayenku, kudin da kuke nema, iyayenku ba zasu ci moriyarsa ba idan sun mutu, ku zauna da su yanzu.
A nan ne na fara kuka, domin na tuna kwana uku ban kira mahaifiyata ba.
3. Suna yin danasani saboda sun ji tsoron fara abin da suke so.
Yace, "Na ga wani malami yana cewa, 'Ina son in bude makaranta ta karatun Al-Qur'ani, amma na ji tsoron mutane su yi min dariya'. Yanzu ya mutu, burinsa ya mutu tare da shi, kada ku ji tsoron mutane, mutane zasu yi dariya yau, gobe su manta, amma ku da burinku zaku tafi kabari tare. Ku fara yau."
Wannan maganar ta daki zuciyata sosai, domin ni ma ina da burin da nake ji tsoron farawa.
4. Suna yin danasani saboda sun boye gaskiya saboda tsoron kada a so su.
Yace, "Na ga mata da yawa sun yi aure da mutanen da basu so ba saboda suna jin tsoron cewa idan sun ce a'a ba za a so su ba. Na ga maza da yawa sun yi shiru a wurin da ya kamata su fadi gaskiya saboda suna son a yabe su. A lokacin mutuwa sai su gane cewa soyayyar da aka gina akan karya ba soyayya bace. Ku fadi gaskiya, ko da za a ki son ku."

5. Suna yin danasani saboda sun manta cewa duniya ba gida bane, hanya ce.
Yace, "Mafi girman nadamar da na gani ita ce, mutane suna gina gida kamar zasu zauna a duniya har abada. Suna tara kudi kamar baza su mutu ba. Amma sai su mutu gidan ya rage. Ku gina lahira. Ku saka wani abu a gaba. Duk abin da kuka bayar a yau, shine zai jira ku gobe."

Bayan ya gama fada, ya yi addu'a ya tafi gida, da asubahi aka kira mu a masallaci cewa Malam ya rasu ya kwanta bai tashi ba, ya mutu cikin barci.
Garin mu baki daya ya rufe da kuka, amma mu matasa bakwai da ya yi wa wannan wa'azin  mun san cewa wannan ce wasiyyar sa ta karshe.

Yau kwana daya kenan da rasuwarsa, amma na riga na kira mahaifiyata, na yafe wa abokina da muke fushi, kuma na fara rubuta littafin da nake ji tsoron rubutawa shekaru biyu.

Ina rubuta wannan labarin ne don kada ku jira sai an yi muku wa'azi a gaban mutuwa. Wa'azi ya zo muku yanzu.

Ku yafe. Ku koma ga iyayenku. Ku fara burinku. Ku fadi gaskiya. Ku tuna lahira.

Allah ya jikan Malam, ya yafe masa yasa Aljannah ce makomarsa damu baki daya.

More Articles by This Writer

Support the Writer

Enjoyed this article? You can support the writer with a voluntary donation.

Your donation supports Muhammed

Minimum donation: $2.00   •   90% of the donation is allocated to the writer after the LodPost commission.

Comments

You must be logged in to post a comment.

About Author

1 Followers
1 Following
5 Articles
6 Likes