Idan kana tunanin samun kudi a online abu ne mai sauki, to ka yi kuskure. Ni ma haka na fara tunani a baya. Ina ganin mutane a TikTok da Facebook suna cewa sun samu N100,000 a rana daya, sai na dauka ni ma zan samu haka cikin sauki. Amma abin da ya faru da ni ya canza min tunani gaba daya.
A watan da ya wuce, na rasa N50,000 dina saboda na fada tarkon "ku ninka kudin ku sau biyu a cikin awa biyu". Wani saurayi ne a Telegram ya turo min sako yana cewa yana da wani bot da idan ka saka N10k zai ba ka N20k a cikin awa biyu kacal. Ya nuna min screenshot na mutanen da ya biya, har bidiyo ma ya turo min. Saboda kwadayi da son samun kudi cikin sauki, na saka N10,000. Bayan awa biyu, ya ce in kara N20,000 don in samu N40,000. Haka na cigaba har kudin da ke hannuna N50,000 ya kare. Daga nan ya toshe ni a Telegram. Kudi ya tafi a banza. Nayi kuka sosai a ranar saboda wannan kudin jarin na jarin business ne danake so nafara.
A ranar ne na gane gaskiya uku da suka canza min tunani kuma suka taimake ni na fara samun kudi na gaskiya a Lodpost.
Gaskiya ta 1: Duk wanda ya ce kawo kudi kafin ka samu kudi, dan damfara ne.
Wannan ita ce babbar darasi da na koya. Aikin online na gaskiya kamar Lodpost, SproutGist, Facebook Monetization, da kuma aikin rubutu duk kyauta ne. Ba sa bukatar ka biya ko sisi. Idan wani ya ce ka biya N2,000 ko N5,000 don a koya maka yadda ake samun kudi ko don a saka ka a wani group, ka gudu kawai. Masu gaskiya suna koya maka kyauta ne sannan suke samu kudi daga nasararka, ba daga kudin ka ba.
Gaskiya ta 2: Samun kudi a online aiki ne, ba sa'a ba.
A baya na dauka zan kwana daya zan samu 10k, na kasa fahimtar cewa dole ne a yi aiki, sai da na yi kwana bakwai ina rubutu a Lodpost kullum ba tare da gajiyawa ba, ina tashi da safe ina rubutu, ina yadawa a WhatsApp groups, ina mayar da martani ga comment, kafin na fara ganin N500 a rana. A rana ta farko views 10 ne kacal na samu. Na ji kunya. Amma yanzu ina samu kullum saboda na hakura ban daina ba. Kudi a online kamar noma ne, sai ka shuka sannan ka jira ya girma.
Gaskiya ta 3: Kar ka fara da abubuwa da yawa a lokaci daya.
Kuskurena na uku shine ina son na yi komai a lokaci daya - TikTok, Lodpost, Crypto, Forex. Na bude dukka a lokaci daya. Duka sun ci ni saboda hankalina ya watse. Sai da na yanke shawara na tsaya akan Lodpost daya tak, na mayar da hankali gaba daya a kanta na tsawon wata daya, na fara samu. Idan kana son samun kudi, ka zabi hanya daya ka yi riko da ita har sai ta fara baka kudi.
Shawarata gare ka da kake karanta wannan yanzu:
Idan kana da N5,000 kacal a hannunka, kar ka saka a wani waje da aka ce zai ninka maka kudin ninki 2. Wannan karya ne. Ka sayi data ka fara Lodpost kamar yadda nake yi yanzu. Ko da N200 ka samu a rana ta farko, kudi ne na gaskiya kuma halal kuma zai karu zuwa N1,000 da N2,000 idan ka cigaba.
Na bude wannan post din ne don kar ka fada ramin da na fada. Na riga na biya kudin kuskure na N50,000 don kai kar ka biya. Kada ka bari kwadayi ya rufe maka ido.
Ka taba fadawa irin wannan damfara ta online? Ka bani labari a Comment kasa, mu koya wa juna kuma mu hana wasu fadawa.
Kada ka manta ka yi SHARE don ka ceci wani dan uwa daga fadawa damfara ta online.
Na Yi Asarar N50,000 A Online Kafin Na Gano Gaskiyar-Karka Fada Cikin wannan Ramin
Support the Writer
Enjoyed this article? You can support the writer with a voluntary donation.
Your donation supports
Muhammed
You must be logged in to post a comment.